OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Harin Jirgin Ƙasa: Yan Ta'adda Sun Saki Ragowar Fasinjoji 23  

Harin Jirgin Ƙasa: Yan Ta'adda Sun Saki Ragowar Fasinjoji 2

Ƴan ta'adda sun saki sauran fasinjoji 23 da suka yi garkuwa dasu a harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna.

 A rahoton da gidan Talabijin na Channels TV ya sanar, sakataren kwamitin da ke kula da harkokin tsaro na ƙasa Usman Yusuf ne ya bayyana hakan.

A cewar Yusuf, ƴan ta’addan sun sako mutanen 23 da suka yi garkuwa da su a ranar Laraba da misalin karfe 4 na yamma.

Ya kuma bayyana cewa kwamitin ya karɓi fasinjojin da aka yi garkuwa da su a yayin harin da aka yi a ranar 28 ga Maris, 2022.

A baya bayan nan ne kuma aka saki rukuni na ƙarshe na fursunonin  a ranar 19 ga Agusta, 2022.

Kafin haka dai ƴan uwan fasinjojin sun gudanar da zanga-zanga da dama da nufin tilastawa gwamnatin tarayya ta shiga tsakani domin ganin an sako ƴan uwansu.

Najeriya na fama da hare-haren ƴan bindiga a ɓangarori da dama na ƙasar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci