OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin Najeriya ta janye umurnin da ta ba wa shugabannin jami'o'i akan su bude makarantu

Gwamnatin Najeriya ta janye umurnin da ta ba wa shugabannin

Gwamnatin Najeriya ta janye umarnin da ta bayar kan cewa mahukunta jami’o’in tarayya da su bude makarantu a cigaba da lakcoci .

Umurnin yana kunshe ne a cikin wata wasika da Hukumar Kula da Jami'o'i ta Kasa (NUC) ta aika mai dauke da kwanan wata 26 ga watan Satumba.

Kamar yadda aka yi wasikar farko ,ta biyu ma na dauke da sa hannun daraktan kudi da asusu na NUC, Sam Onazi, a madadin sakataren zartarwa, Abubakar Rasheed.

Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ne hukumar ta umurci shugabannin jami’o’in gwamnatin tarayya da su bi umarnin kotun masana’antu ta kasa (NIC) akan umurnin da ta bawa mambobin kungiyar ASUU da su janye yajin aiki su bude makaranta,ba tare da kammala tantance muhimman batutuwan da suke bukata ba.

Gwamnati ta bukaci shugabannin jami'o'i da mataimakansu da su tabbatar da cewa an bude makaranta malaman da ke yajin aikin sun dawo an cigaba da karatu.

Wannan Umurni da gwamnati ta bayar ya haifar da rudani ga hukumomin jami'o'i yayin da shugabannin jami’o’in ba su san ta inda za su fara ba.

Sai dai sabuwar wasikar da NUC ta aikawa shugabannin jami’o’in tarayya mai dauke da lambar tambari "Janyewa na Ref: NUC/ES/138/ Vol.64/135 Kwanan wata 26 ga Satumba 2022."

Sabuwar wasiƙar mai dauke da lambar tambari NUC/ES/138/Vol.64/136 da kwanan wata 26 Satumba, tana cewa; “An umurce ni da in janye batun wancan wasikar ta farko mai tambari Ref, NUC/ES/138/Vol.64/135 mai dauke da kwanan wata 26 ga Satumba 2022 kan wannan batu na yajin aiki Sakamakon haka, an janye wannan batu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci