OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamna Radda ya zargi wasu mutane da samun riba da ayyukan ta'addanci

Gwamna Radda ya zargi wasu mutane da samun riba da ayyukan t

Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda, ya zargi wasu jami’an gwamnati da jami’an tsaro da taimakawa ayyukan ta'addanci a kasar nan. 

 

Radda yace wasu tsirarun mutane suna cin riba da ayyukan ta'addanci da yayi kamari a jihar shiyasa aka kasa dakile matsalar.

 

Da yake magana a gidan Talabijin na Channels TV a ranar Juma’a, gwamnan ya bayyana cewa, “’ta’addanci ya rikide ya zama tamkar wata sana’a mai riba, inda ya hada da daidaikun mutane a cikin gwamnati, hukumomin tsaro, da kananan hukumomi.”

 

Ya kuma jaddada cewa, bawai alamuran siyasa ne suke ta'azzara matsalar tsaro ba kamar yadda ake tunani.

 

 Gwamnan ya bayyana cewa matasa da dama a yankin Arewa ana yaudarar su da ‘yan kudin da basu wuce Naira 500 ba su fada alamuran ta'addanci.

 

Gwamna Radda ya bayyana cewa an gayyace su birnin Washington su halarci wani taro game da matsalar taro.

 

 Ya kara da cewa tafiyar ta baiwa gwamnonin karin haske kan rashin tsaro a yankin. “Taron ba wai na gwamnonin da aka zaba na jihohin Arewa ba ne, a’a, an yi taron ne a cibiyar nazarin zaman lafiya ta Amurka. An gayyace mu da mu zauna da su domin mu samar da mafita mai ɗorewa ga matsalolin da ke addabar al’ummarmu".

 

 A cikin 'yan shekarun nan, an yi ta samun tashe-tashen hankula na hare-haren 'yan bindiga da ke faruwa akai-akai, musamman a yankunan karkara.

 

Wadannan hare-haren sun haifar da yawaitar sace-sacen jama'a da kashe-kashen da ba su ji ba ba su gani ba, lamarin da ya haifar da cikas ga harkokin kasuwancinsu da na yau da kullum.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci