Kwamishinan tsare-tsare da Kasafi, Nura Muhd ƊanKadai
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa zata tabbatar da wadatar abinci tare da samarwa Fulani makiyaya matsuguni a jihar domin magance matsalar makiyaya/manoma.
Kwamishinan tsare-tsare da Kasafi, Alhaji Nura Muhd Ɗankadai ne ya sanar da haka lokacin da yake ƙarin haske kan kasafin kudin bana a ɗakin taron ma'aikatar dake sakateriyar Audu Bako.
Ya ce gwamnati ta warewa ɓangaren noma Naira biliyan 5 da miliyan takwas a kasafin na bana domin cimma hakan.
Kwamishinan jihar, Alhaji Nura Muhammad Dan Kadai ya ce an ware Naira 100,000,000 domin gina ƙauyen Fulani makiyaya a jihr.
Ya ƙara da cewa za'a samar da wurin ajiye dabbobi da hanyoyin kiwo da kuma dam domin dabbobin a kan Naira 40,000,000.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na daga cikin gwamnonin dake ganin akwai buƙatar Fulani makiyaya su samu matsuguni domin rage hatsarin da sukan tsinci kan su a wasu sassan ƙasar nan dama samarwa ƴan ƴan su ilimi.
Jaridun kasar nan sun rawaito Gwamnan a mabanbanta lokuta yana cewa hakan zai tabbatar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.
0 Tsokaci