OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Ma'aikatan Kaduna Sun Yi Murna Yayin Da El-Rufa'i Ya Basu Kyautar N1.38bn

Ma'aikatan Kaduna Sun Yi Murna Yayin Da El-Rufa'i Ya Basu Ky

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa'i| Hoto Daga: BBC

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya amince da kashe sama da naira biliyan daya a matsayin alawus na karshen shekara ga ma'aikatan gwamnati.

Mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye ne ya bayyana hakan a ranar Talata.

Adekeye ya ce ma’aikatan za su samu karin kashi 30 zuwa 100 na albashin su.

Adekeye ya kara da cewa za a kashe wa ma’aikatan N1.382 a matsayin alawus na karshen shekara.

Ya kara da cewa wannan ci gaban ya samo asali ne sakamakon kokarin da gwamnati ke yi na inganta jin dadin ma’aikatan jihar.

Ya ci gaba da bayyana cewa, “Ma’aikata daga mataki na 1-7 ne za a biya su kashi 100 na albashin su na wata a matsayin kari. Ma’aikatan gwamnati daga mataki na 8-13 za su samu kashi 40 cikin 100, yayin da manyan jami’an da ke mataki na 14 zuwa sama za su samu kashi 30 cikin 100 na albashinsu na wata-wata.”

Adekeye ya bayyana cewa jihar Kaduna ce ta farko da ta fara biyan mafi karancin albashi a shekarar 2019 tare da kara mafi karancin albashin 'yan fansho na wata-wata zuwa 30,000.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci