OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin Borno Ta Tabbatar Da Shirin Sake Gina Gudumbali

Gwamnatin Borno Ta Tabbatar Da Shirin Sake Gina Gudumbali

Borno state governor, Babagana Umara Zulum| Photo Source: PremiumTimes

Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da shirin ta na sake gina Gudumbali, wanda a da can ke hannun 'yan Boko Haram kuma sojojin Najeriya suka kwato.

Sanarwar ta fito ne daga bakin kwamishinan sake gine-gine, gyara da sake tsugunar da jama’a na jihar Borno Engr. Mustapha Gubio.

Gubio wanda ya ziyarci garin a karamar hukumar Guzamala ta jihar ya ce gwamnati ta dukufa wajen sake gina garin tare da sake tsugunar da mazauna garin musamman yanzu da aka kwato garin.

Idan dai ba a manta ba gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bukaci sojojin da su tabbatar da kwace garin a wani lokaci a watan da ta gabata domin baiwa gwamnatinsa damar aiwatar da sake tsugunar da mazauna garin.

Jama’a sun bar garin bayan harin Boko Haram a shekarar 2014.

Sai dai a shekarar 2018, an sake tsugunar da su amma daga baya aka tilasta musu barin garin bayan wani harin da Boko Haram suka kara kaiwa. 

A cewar Kwamishinan: “Mun gudanar da tantance matakin barna a Gudumbali.

“Kamar yadda shugaban kwamitin ya ce za mu koma mu mika rahoton ga gwamna domin a fara aikin sake ginawa.

"Bayan haka, aikin sake tsugunarwa zai biyo baya."

Gubio ya kara jaddada bukatar samar da tsaro domin a samu nasarar sake gina garin tare da tsugunar da jama’a.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci