OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Festus Keyamo: Zan iya tafiya daga Abuja zuwa Kaduna ba tare da 'yan rakiya ba

Festus Keyamo: Zan iya tafiya daga Abuja zuwa Kaduna ba tare

Karamin ministan kwadugo Festus Keyamo ya bayyana cewa kamar yadda ko wa ke iya bin hanyar kaduna zuwa Abuja shima ba bu abinda zai sa ba zai iya bi ba. 

Kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels TV inda aka tambayeshi ko zai iya tafiya a mota duk da kalubalen tsaro, karamin ministan ya amsa da cewa: “ko wa na yi, nima zan iya yin hakan.

"Na gani a labarai a makon da ya gabata cewa wai ni na ce Buhari ya kawo karshen matsalar rashin tsaro.

"Ni ban fadi haka ba, yanzu lokaci ne da ake yada labarun karya.

"Abinda nake nufi munzo mun tarar da matsalar Boko Haram a arewa maso gabas.

"Iyakacin abinda na fada kenan amma aka min kari cewar na ce mun samu matsalar Boko Haram da rashin tsaro a fadin kasar.

"Gwamnati tayi kokarin kawar da Boko Haram a arewa maso gabas, ba kuma wai ya kare gaba daya ba, amma dai anci karfin su.

“Hanyar Damboa zuwa Chibok a yanzu an iya bi.

"Batun rikicin manoma da makiyaya ya yi kamari tsakanin shekarar 2017 zuwa 2020 Hukumar ta'addanci ta duniya ta bayyana haka Ba ni na fada ba.

"Hukumar ta kuma ce hare-haren sun ragu matuka a shekarar 2021.

"Sannan kuma ya sake raguwa a 2022.

"Saboda  haka an samu sauki ta fuskar rikicin manoma da makiyaya."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci