OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Fataucin miyagun kwayoyi: tsohon Dan wasan kwallon kafa ya shiga hannu

Fataucin miyagun kwayoyi: tsohon Dan wasan kwallon kafa ya s

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) sun kama wani tsohon dan wasan kwallon kafa, Okafor Emmanuel Junior.

An kama Junior ne dai a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, a lokacin da ya taso daga Sao Paulo, Brazil, ta hanyar Addis Ababa, Ethiopia.

Ya hau wani jirgin saman Habasha dauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram 1.40 ya boye a cikin jakunkuna.

An kama matashin mai shekaru 33 dan asalin karamar hukumar Arochukwu ta jihar Abia ne a ranar Litinin 26 ga watan Satumba, bayan da jami’an yaki da safarar miyagun kwayoyi suka gano cewa ya boye hodar iblis dinne a hannun jakunkunan.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja, a yayin wata tattaunawa da aka yi da shi.

Okafor ya bayyana cewa tsohon dan wasan kwallon kafa ne da yake buga wa kungiyar kwallon kafa ta asibitin koyarwa na jami’ar Enugu, inda ya yi wasa har na tsawon shekaru hudu kafin ya tafi kasar Sri Lanka a cikin shekarar 2014.

"Ya kara da cewa ya koma Brazil ne daga Sri Lanka bayan ya buga wasa na tsawon shekaru biyu amma ya kasa ci gaba da wasan kwallon kafa a Brazil saboda rashin takardun shaidar zama a hukumance," in ji Babafemi.

Wani dan kasar Brazil da ya dawo, Ibeh Chinedu Damian, an kama shi ne a ranar da ya isa filin jirgin sama na Legas daga Sao Paulo ta Brazil ta jirgin kasar Habasha.

An gano Ibeh wanda ya fito daga Ahiazu, karamar hukumar Mbaise ta jihar Imo, ya boye bakar hodar ibilis mai nauyin kilogiram 3.20 wanda aka fi sani da ‘Lucci’ a cikin jakunkunan sa na bogi guda biyu.

A cikin bayanin sa, ya ce za a biya shi N3.1m domin samun nasarar shigar da hodar iblis din  cikin Najeriya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci