OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Fashewar Bam Yayi Sanadiyar Rasa Sojoji 3 A Katsina

Fashewar Bam Yayi Sanadiyar Rasa Sojoji 3 A Katsina

Bayan fashewar wani bam a karamar hukumar Danmusa dake jihar Katsina, an kashe sojoji uku.

An kashe sojojin ne da wata bam da ‘yan ta’adda suka binne.

Motar da ke dauke da sojojin da ke aiki na musamman ta taka bam din da yayi sanadiyar mutuwar su.

Kamar yadda AllNews ta tattaro, wata majiya ta bayyana wa Leadership cewa an garzaya da sauran sojojin da suka samu raunuka sakamakon fashewar bam din zuwa asibiti domin samun kulawa ta musamman.

Majiyar ta bayyana cewa, “Su (sojojin) suna kan hanyarsu ne daga Mara zuwa Kaiga kafin a yi musu kwanton bauna ta hanyar dasa bam din."

Majiyar ta kara da cewa daya daga cikin Sojojin da suka mutu ya kone da motar sintirin tasu.

Sai dai har yanzu rundunar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci