OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Cutar Kwalara Ta Kashe Mutum Daya, 13 Suna Asibiti a Taraba

Cutar Kwalara Ta Kashe Mutum Daya, 13 Suna Asibiti a Taraba

Barkewar cutar kwalara a yankin Jen-Ardido da ke karamar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba tayi sanadiyar mutuwar mutum daya da kwantar da 13.

 

A ranar Alhamis ne Shugaban karamar hukumar, Markus Hamidu ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Hamidu yace mutum daya ne ya mutu a ranar Laraba tare da kwantar da 13 a asibiti.

 

Ya kara da cewa ana kan kulawa da wanda suka kamu da cutar tare da kokarin ceto su.

 

Yayin da yake tabbatar da lamarin, yace babu wani bayanin da ya nuna an kara rasa rai ko karuwan yaduwar cutar sakamokon ma'aikatan lafiya na kokarin hana yaduwar ta.

 

Hamidu ya jajanta wa wadanda abin ya shafa kuma tare da cewa baza a nade hannu ba wajen yaki da cutar.

 

Ya kara da cewa har yanzu babu masaniya akan abinda ya jawo barkewar cutar.

 

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci