OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ba zan biya malaman jami'a da suka shiga yajin aikin ASUU ba – Gwamnan Taraba

Ba zan biya malaman jami'a da suka shiga yajin aikin ASUU ba

Governor Darius Ishaku of Taraba State

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku ya ce ba zai biya malaman jami’ar jihar Taraba da ke yajin aiki a karkashin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ba.

Ishaku ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a Taraba yayin da ake gudanar da taron kwata na uku na kungiyoyin TAKAN da ECWA.

Kamar yadda jaridar Blueprint ta ruwaito, gwamnan ya ce malaman jami’o’in ba su da dalilin shiga yajin aikin ASUU.

Ya kara da cewa dole ne malaman su girbi abin da suka shuka.

A cewar sa: “Mu manyan ana zargin mu ne da tura 'ya'yan mu zuwa kasashen waje karatu da kuma lokacin da muka bukaci malaman mu da su koma aji domin yaran talakawa su samu ilimin sai suka ki yarda."

Ya kuma kara da cewa, da tsarin da gwamnatin sa ta kafa, duk wata gwamnati mai ci za ta fi amfana.

Ishaku ya kuma yi kira ga kiristoci da su kasance da hadin kai yayin da ya kara da cewa gwamnatin sa na aiki da kowa ba tare da la’akari da kabila ba.

Ya kuma yaba da yadda kungiyar kiristoci ta taka rawa wajen ganin ya zama gwamnan jihar tun shekarar 2015.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci