OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Buhari Zai Halarci Babban Taron Zuba Jari Na Saudiya A Yau

Buhari Zai Halarci Babban Taron Zuba Jari Na Saudiya A Yau

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai halarci taron zuba jari na Saudiyya a Riyadh.

Taron wanda Cibiyar Future Investment Initiative ta shirya, zai samu wakilci daga kasashe daban -daban na duniya.

An bayyana hakan ne ga manema labarai a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu.

Shehu ya ce shugabannin kasuwanci da masana’antu, ma’aikatan banki, da kwararru kan makamashi daga Najeriya za su bi sahun shugaban a taron.

Taron na bana zai dauki tsawon kwanaki uku tare da taken, "Zuba Jari akan Dan Adam."

Shugabannin a bugu na 5 na babban taron saka hannun jarin, za su tattauna batutuwa kan makomar saka hannun jari a duk duniya.

Wasu batutuwan da za a tattauna sun haɗa da ci gaba akan makamashi, kimiyya, tasirin sauyin yanayi da sauran su.

Wadanda zasu raka shugaban a cewar sanarwar sun hada da, “Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, farfesa Isa Ibrahim Pantami, karamin ministan harkokin waje, Ambasada Zubairu Dada, karamin ministan albarkatun man fetur, Cif Timipre Sylva, mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), darakta janar na hukumar leken asiri ta kasa, Ambasada Ahmed Rufa'i Abubakar, manajan darakta na hukumar saka hannun jari ta Najeriya, Uche Orji da shugaban 'yan Najeriya a hukumar kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa .

"Wasu mahalarta daga kamfanoni masu zaman kansu sun haɗa da Alhaji Mohammed Indimi, Alhaji Aliko Dangote, Tope Shonubi, Wale Tinubu, Alhaji Abdulsamad Rabiu, Hassan Usman, Omoboyode Olusanya, Abubakar Suleiman, Herbert Wigwe da Leo Stan Ekeh."

 

Sanarwar ta kuma kara da cewa shugaban zai dawo Najeriya a ranar Juma'a bayan yin aikin umarah a kasa mai tsarkin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci