OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 11 Watanni da suka shude

Ina Tausayawa Shugaban Ƙasa Mai Jiran Gado - Sanusi Lamiɗo

Ina Tausayawa Shugaban Ƙasa Mai Jiran Gado - Sanusi Lamiɗo

Tsohon Sarkin Kano kuma mataimakin shugaban hukumar bunƙasa zuba jari ta Kaduna, Lamido Sanusi, ya nuna tausayawansa ga shugaban da zai gaje Muhammadu Buhari.

Khalifa Sunusi ya bayyana haka ne a Kaduna ranar Asabar a lokacin da yake jawabi ga fitattun ƴan siyasa a wani shirin zuba jari na Kaduna mai taken, “Gina tabbataccen tattalin arziƙi”.

Sunusi wanda shine Sarkin na 14 ya ce tattalin arziƙin Najeriya ya danganta ne da ɓangaren mai da iskar gas da kuma cire tallafi, cewar Jaridar Punch.

“Najeriya na ci gaba da zama ƙasar bashi, Ba don ci gaba ba sai dai a matsayin bashi, da kuma masu mulki zama masu arziƙi da mayar da su hamshakan attajirai dare daya.

“A shekarar 2023, idan muka yi zaɓe, ba za mu iya ci gaba da gudanar da harkokinmu ba.  

"Domin duk wani ci gaban ƙarɓan bashi zai haifar da rashin tsaro kuma zamu iya komawa kamar Mali, da Burkina Faso.

“Ba za mu iya ci gaba da matsawa gaba ba;  dole ne mu dawo muyi gyara,” inji shi.

Yayin da yace yana tausayin shugaban da zai gaji gwamnatin nan duba da yadda harkan tattalin arziƙi ya taɓarɓare.

Ya ci gaba da cewa, kudin biyan bashin da ake bin Najeriya da gwamnatin tarayya ya kai Naira tiriliyan 2.597 yayin da kuɗaɗen shiga ya kai Naira tiriliyan 2.4.

“Mun ga matsalar kuma za mu ci gaba da gani, ina   tausayin shugaban da zai zo a watan Yuni ya ce zai cire tallafin man fetur,” .

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai