OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 11 Watanni da suka shude

Buhari Ya Amince Da Bayar Da Ton 12,000 Na hatsi Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa

Buhari Ya Amince Da Bayar Da Ton 12,000 Na hatsi Ga Wadanda

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da fitar da ton 12,000 na hatsi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a fadin kasar nan.

 Darakta-Janar na Hukumar bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Mustapha Habib Ahmed, ne ya bayyana hakan a Abuja jiya a yayin bikin Ranar Rage Hadarin Bala’i ta Duniya na 2022.

Ya ce NEMA tana cigaba da rarraba kayan agajin gaggawa ga wadanda abin ya shafa.

Daraktan ya kara da cewar "duk da ambaliyar ruwan da aka yi a Lokoja ta Jihar Kogi tana shafar jigilar kayayyakin, an sanar da jami’an tsaro don tabbatar da an samu nasarar isar da kayayyakin"

Shugaban NEMA ya Kuma zargi cewar babban illar da bala’in ambaliyan ya yi a fadin kasar nan a bana ya faru sanadin Watsi da gargadin da hukumar tayi tun da farko. 

 Ya ce gwamnatin tarayya ta sanar da jahohi da kananan hukumomin kasar game da hatsarin ambaliya tare da yin amfani da taswirorin kasada wajen gano wuraren da abin ya shafa, amma ba a kula da gargadin ba.

Ministar harkokin jin kai da kula da bala’o’i da ci gaban Al'umma, Sadiya Umar-Farouk, wanda Darakta a sashin jin kai Ali Grema ya wakilta, ta ce za a iya kwatanta girman barnar da ambaliyar ruwa ta yi a bana kawai da ta shekarar 2012.

Ta bukaci al’umma da su dauki hasashen yanayi da gargadin ambaliya da muhimmanci, domin gujewa faruwar hakan a nan gaba. 
 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai