A jiya Larabar da ta gabata ne gamayyar kungiyoyin farar hula (CCSOs) suka mamaye titunan Abuja domin nuna rashin jin dadinsu kan abin da suka bayyana a matsayin ‘ci gaba da cin mutuncin jakuna da ‘yan kasashen waje mazauna kasar nan ke yi.
A cewar kungiyar, wannan danyen aikin na ci gaba da gudana duk da umarnin gwamnatin tarayya da majalisar dokokin kasar.
Da yake jawabi yayin gangamin, shugabannin gamayyar kungiyoyin Barr. Emmanuel Onwudiwe da Comrade (Engr) Ogwuche Emmanuel, sun ce: “Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 21 ga watan Maris, 2022, bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya ya ba da umarni cewa baƙi basu da damar shiga daji kai tsaye don saye ko yankan jakuna kai tsaye ba,”
"Haka kuma Shugaban kasar ya kaddamar da wani kwamiti a karkashin jagorancin Suleiman Audu tare da umarnin aiwatar da dokar hana baki sayen kayan gona kai tsaye daga kofar gonakin."
Gammayar kungiyoyin Farar hular sun kuma kara da cewar " Ministan Noma, Dr Mohamed Mahmood Abubakar bashi da hurumin cigaba da bai wa ‘yan kasar China izinin shiga daji da yin mu’amala kai tsaye da manoma da masu sana'ar saida Jaki domin yin hakan ya saba da umarnin da Shugaban kasar ya bayar kai tsaye"
Kungiyoyin Farar hular sun bayyana cewar saida Jaki ga kasashen Waje zai iya kawo ribar akalla Naira biliyan 60 cikin tattalin arzikin Najeriya ta hanyar zuba jari kai tsaye sannan kuma zai iya samawa ‘yan Najeriya sama da 250,000 matukar aka tsara harkar siye da siyarwar Jaki ta hanyar daya dace don biyan bukatun Yan Najeriya.
Saboda haka Masu zanga-zangar sun bukaci Gwamnatin ta Maida hankali wajen karfafa fannin domin zakulo kasar daga durkushewar tattalinarzikin da ke kawo mata farmaki.
0 Tsokaci