OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Buhari Ya Sha Alwashin Dakile Masu Tada Zaune Tsaye, Yayin Da ake Kokarin Dawo da Igboho

Buhari Ya Sha Alwashin Dakile Masu Tada Zaune Tsaye, Yayin D

Shugaba Muhammadu Buhari| Hoto Daga: Facebook

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa za a kara himma don zakulo wadanda ke tada zaune tsaye da kuma takurawa yan kasa.

Shugaban ya bayar da tabbacin ne jim kadan da aka damke wani shugaban masu fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho.

Hukumar 'Yan Sanda ta Kasa da Kasa (Interpol) ne ta kame Igboho a Cotonou, Jamhuriyar Benin.

Shugaban kasan, wanda bai yi magana kai tsaye ba game da damke Igboho, ya ba da tabbacin a gidansa da ke Daura, Jihar Katsina, bayan Sallar Idi, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban a makonnin da suka shude, ya yi barazanar tunatar da masu laifi da masu neman ballewa “A cikin yaren da suke fahimta”.

Bayan wannan bayanin da Shugaba Buharin yayi ne ta haifar da kwamuso Shugaban kungiyar ‘yan awaren nan na fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB).

A cikin wata sanarwa da hadiminsa na yada labarai, Garba Shehu ya fitar, an ruwaito Buhari yana umartar jami'an tsaro da su zama masu jajircewa wajen wanzar da zaman lafiya a kasar tare da tabbatar da kyakkyawar dangantaka da al'ummomi ta yadda za su iya karbar bayanan sirri.

Kalaman na Buhari sun zo ne yayin da gwamnatin tarayya ta fara yunƙurin kammala tsare-tsaren dawo da Igboho wanda shi da matarsa ke tsare a hannun jami'an tsaro.
Matar Igbohon, Ropo, yar kasar Jamus ce wacce aka tsare a kan hanyarsu ta zuwa Jamus.

Ma’aikatar Tsaron Jiha ta sirri (DSS) ta bayyana cewa tana neman Igboho ruwa a jallo bayan da jami’anta suka kai samame gidan sa da ke garin Soka. 

A yayin samamen, DSS ta ce ta kwato alburusai da kayan tsafe-tsafe,  kuma ta kama mutane 13 da kashe wasu biyu.

Wata kara da wasu abokan hulda 12 na Igboho suka shigar, wacce aka ruwaito an tsayar domin saurarar ta a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar Talata ba ta yiwu ba yayin da kotuna ke gudanar da hutun babban sallah.

An shigar da kara ne game da neman hakkin dan adam biyo bayan ci gaba da tsare mutanen 12 bayan da DSS suka kama su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci