OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Buhari Ya Karbi Bakuncin 'Yan Majalisa Tare Da Yaba Musu

Buhari Ya Karbi Bakuncin 'Yan Majalisa Tare Da Yaba Musu

Shugaba Muhammdu Buhari| Hoto Daga: Shafin Shugaban na Facebook

A ranar talata me Shugaba Muhammdu Buhari ya karbi bakuncin 'yan majalisar tarayya a liyafar cin abincin dare a Abuja.

A wata sanarwa dauke da sa hannun mai ba shugaban kasan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, shugaban ya yabawa 'yan majalisan ne "saboda sauke nauyin da suka rataya a wuyansu na yin doka cikin dattako da cancanta, yana mai bayyana majalisar a matsayin 'cikakkiyar kawa ta ci gaban kasa."

Yayin da yake lura da muhimmiyar rawar da Majalisar Dokoki ta Kasa ta taka, ya ce, "ikon mu na yin mulki don amfanin mutanen Najeriya ya dogara ne da babbar yarjejeniyar hadin kai da kawance tsakanin Majalisar Dokoki da na Zartaswa."

Ya kara da cewa, "aikin bincikar aiyukan  junan mu ba gayyatar rikici ba ne ko kuma nuna rashin jituwa, musamman lokacin da kulla da yarjejeniya da sasantawa suka tabbatar da zama hanya mafi inganci."

Yayin da yake yabawa majalisar, ya ce, "Kun banbance kanku ne ta yadda kuke gudanar da aiki a ofis, ta hanyar ingancin bayani da kuke yi a majalisar, da kuma karfin da kuke da shi na tinkarar matsaloli masu wuya da kasar ke fuskanta cikin dattaku da iyawa."

Shugaban ya nuna sadaukarwa don ci gaba da hadin gwiwa da kawance tsakanin sa da Majalisar.

A cewar sanarwar, "Shugaban ya ce yana fatan ci gaba da aiki tare da hadin gwiwa tsakanin bangaren zartarwa da na bangaren dokoki na gwamnati, tare da aiki tare don cimma manufa daya ta zaman lafiya da ci gaban kasa."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci