OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Buhari Ya Ji Dadin Kame Da Kwato Hodar Ibilis Da Hukumar NDLEA Tayi

Buhari Ya Ji Dadin Kame Da Kwato Hodar Ibilis Da Hukumar NDL

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nuna jin dadin sa kan yadda hukumar NDLEA ta yi nasarar kamawa da tarwatsa wata kungiyar ta’ammali da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa a Jihar Legas. 

Hukumar NDLEA ta yi nasarar kwato kilogiram 1,855 na hodar iblis da darajar su ta kai dala miliyan 278.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.

A cewar sa, shugaban ya bayyana farin cikin sa ne a wata wayar tarho da ya yi da shugaban hukumar ta NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, daga New York.

A halin yanzu dai shugaban yana birnin New York na kasar Amurka, inda yake halartar taro na 77 na Majalisar Dinkin Duniya (UNGA77).

Shugaban ya bayyana cewa labarin nasarar kamen ya burge shi.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito, Buhari ya ce: “Ina matukar jin dadin aikin da kuka bayar wajen kawar da matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi.

“Yana faranta min rai yayin da nake ci gaba da bin nasarorin da aka samu a karkashin jagorancin ku.

“Kun nuna sau da yawa cewa zabar ku don jagorantar wannan yaƙin da miyagu ƴan kasuwancin mutuwa waɗanda kawai manufarsu ita ce yi wa matasanmu barazana da kuma dagula makomar matasan mu, zaɓi ne mai kyau.

"Don Allah ku ci gaba da aiki mai kyau."

Adesina ya ci gaba da cewa shugaban kasar yana mai cewa: “Buba Marwa yana aiki mai kyau. Ton biyu na hodar iblis, shi ne magana."

Hukumar NDLEA ta sanar da babban kame a tarihi na hodar iblis da ta kai sama da dala miliyan 278 tare da kama masu safarar miyagun kwayoyi ciki har da wani dan kasar waje a wani babban samame da aka kwashe kwanaki biyu ana yi a wurare daban-daban a Legas.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci