OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Buhari Ya Sake Alkawarin Ƙara Ƙaimi Wajen Daƙile Matsalar Tsaro

Buhari Ya Sake Alkawarin Ƙara Ƙaimi Wajen Daƙile Matsalar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, a Legas, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi imani da karfin sojojin Nijeriya na samar da dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

 Da yake bayyana buɗe gasar wasannin sojojin ruwa na Najeriya karo na 12 a birnin Legas, shugaban ƙasar a wata sanarwa da kakakin shugaban sa, Femi Adesina ya fitar, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa rundunar sojin kasar za ta ci gaba da gudanar da ayyukansu  domin daƙile kalubalen tsaro a kasar.

Shugaban kasan ya kara da cewar Wasanni hanya ce ta karfafa dangantakar da ke tsakanin sojoji, da horar dasu akan shirye-shiryen yin aiki tare.

Ya Kuma ce yana da yakinin cewa wadannan wasannin za su haifar da dandali ga sojojin ruwan Najeriya don cimma wadannan manufofi da sauransu.

 Ya ce hukumomin tsaro za su ci gaba da tabbatar da cewa an samar da dukkan matakan da suka dace domin kare lafiyar ‘yan Najeriya.

Shugaban ya kuma sake jaddada mahimmancin hadin gwiwa tsakanin sojoji da sauran hukumomin tsaro da sauran al’umma domin wanzuwar zaman lafiya da tsaro.

Yayi bikin Shugaba Buhari ya kaddamar da sabon wajen wasannin motsa jiki na sojojin ruwa da aka gina a kwanan baya, ya yabawa babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo, bisa yadda yake saka hannun jari wajen gina harkokin wasanni.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci