OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Borno: Imam Babakura Ya Kaubuta Daga Hannun 'Yan Boko Haram

Borno: Imam Babakura Ya Kaubuta Daga Hannun 'Yan Boko Haram

Alkali Babakura Imam

Tsohon ma'aikacin gidan talabijin na Najeriya (NTA) kuma ma'aikacin International Rescue Committee (IRC), Alkali Babakura Imam ya kubuta daga hannun 'yan Boko Haram.

Kungiyar ISWAP ta bangaren Boko Haram ta sace Imam a ranar 10 ga watan Maris na 2022 lokacin da suka kai hari Monguno.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Imam ya sami ‘yanci a yammacin jiya (Talata), inda ya kara da cewa yana cikin koshin lafia.

Wani dan uwa da ya ji daɗin sakinsa ya ce: “Bayan ya shafe kwanaki 174 a tsare, Babban Manajan yanki na IRC ya samu ’yancin sa.”

A cewar wata majiyar tsaro da ta nemi a sakaya sunanta, Imam a halin yanzu yana hannun su (jami'an tsaro) kafin a hada shi da iyalan sa.

Majiyar ta ce: “Yanzu haka yana ofishin mu a nan Maiduguri ana daukan bayan sa da duba lafiyar sa kafin a hada shi da iyalansa daga baya."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci