OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Bankin Raya Kasashen Musulunci Ya Nuna Damuwa Kan kan Yawan Yaran Da Basu Zuwa Makaranta A Arewacin Najeriya

Bankin Raya Kasashen Musulunci Ya Nuna Damuwa Kan kan Yawan

Bankin Raya Musulunci ya ce adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Arewacin Najeriya yana da matukar damuwa kuma tuni aka fara tattaunawa kan bullo da hanyoyin da za a taimaka wajen magance matsalar.

Shugaban bankin, Dr. Muhammad Sulaiman Al-Jasser ya bayyana haka a daren ranar Talata a Kano yayin da yake amsa tambayoyi yayin wata ganawa da manema labarai da ya gudanar tare da mataimakin gwamnan jihar, Dr. Nasir Yusuf Gawuna a gidan gwamnati.

Al-Jasser ya ziyarci Kano ne domin kaddamar da dakin gwaje-gwajen kula da dabbobi, da rarraba kayan aikin karfafawa kananan manoma da kuma duba aikin fadada madatsar ruwa na Watari, wanda bankin ya bada tallafin dala miliyan 95 domin shirin inganta aikin noma da kiwo na jihar Kano (KSADP).

Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban bankin a safiyar yau, ya bukaci bankin da ya tallafa wa fannin ilimi, musamman yara mata, Almajiri da kuma yaran da ba su zuwa makaranta, yayin da ya kuma yaba da tallafin da gudummawar da bankin ke bayarwa wajen rage radadin talauci da sauran ayyuka tare da taimakon inganta yanayin rayuwar kasashe mambobinsa.

Sai dai da yake amsa tambayoyin manema labarai kan ko bankin na duba matsalar almajirai da rashin zuwa makaranta a Kano da Arewacin Najeriya, shugaban bankin ya bayyana cewa suna matukar sha’awar taimakawa yaran da ba su zuwa makaranta.

Shugaban bankin ya shaida cewa suna hada hannu da gwamnati wajen kaddamar da Wani tsari da ake kira Smart Education domin Tallafawa yaran da basa zuwa Makaranta da inganta ilimi a Nigeria.

Al jassar Ya ce idan kasar ta zo da tsarin ayyuka masu inganci, bankin a shirye yake ya taimaka "Muna son taimakawa wadanda suka taimaki kansu," in ji shi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci