OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Tsaunin Dikko ya murkushe Almajirai takwas har lahira

Tsaunin Dikko ya murkushe Almajirai takwas har lahira

Kimanin Almajirai takwas suka rasu sakamakon ruftawar wani yanki na tsaunin Dukku da ke unguwar Badariya a cikin Birnin Kebbi a jihar Kebbi. 

 

Malamin makarantar Malam Dan Umma, yace lamarin ya faru ne a ranar Asabar din da ta gabata.

 

Yace "kawai ina cikin gida sai naji ihun alumma ina zagayawa bayan gida na tarar wani bangaren tsaunin ya rufta akan daliban ya danne su"

 

Almajirai takwas daga cikinsu nan take suka rasu yayin da aka ceto daya daga cikin baraguzan da ya samu munanan raunuka.

 

Mallam Umma ya ce, tsaurin a bayan wurin da Yake zaune da almajiransa yake kuna sukanyi amfani da shi a matsayin bandaki, ko kuma su debi kasar domin sun ginawa kansu dakuna.

 

Jama’ar yankin sun yi dafifi a wurin da abun ya faru suna jajanta wa malamin. An yi jana’izar wadanda suka mutu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

 

 A halin da ake ciki, shugaban karamar hukumar Birnin Kebbi, Alhaji Dahiru na Yaya, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana hakan a matsayin wata kaddara daga Allah, tare da addu’ar Allah ya jikan su da rahama.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci