OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Bankin duniya zai kula da lafiyar mutane biliyan 1.5

Bankin duniya zai kula da lafiyar mutane biliyan 1.5

Bankin Duniya ya bayyana shirin tabbatar da ingancin kiwon lafiya mutane biliyan 1.5 daga nan zuwa shekarar 2030. 

 

Wannan yunƙurin wani ɓangare ne na tsarin bankin na daidaita tsarin kula da lafiyar Alumma tsakanin kowane mataki na rayuwa, tun daga ƙuruciya har zuwa girman mutum.

 

Tun da fari dai bankin yana da tarihin tallafawa ayyukan kiwon lafiyar mata da yara a ƙasashe sama da 100 a fadin duniya.

 

Ajay Banga, shugaban bankin duniyar, ya jaddada yanayin hadin gwiwa na wannan aiki, yana mai bayyana muhimmiyar rawar da hadin gwiwa tsakanin bankin da kamfanoni masu zaman kansu ke takawa wajen fadada damar samar da ingantaccen kiwon lafiya ga dubban alumma.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci