OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ASUU: SERAP, Dalibai Sun Kai Shugaba Buhari Kotu Akan Tsawaita Yajin aikin

ASUU: SERAP, Dalibai Sun Kai Shugaba Buhari Kotu Akan Tsawai

Kungiyar lauyoyi ta SERAP da daliban jami’o’i 5 sun maka shugaban kasa Muhammadu Buhari kara akan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) ta ke yi.

Daliban da kungiyar ta SERAP su bukaci kotu ta ayyana rashin amincewar gwamnatin tarayya ta biya bukatun ASUU, wanda ya janyo tsawaita yajin aikin da kuma take hakkin daliban na samun ingantaccen ilimi a matsayin haramun.

Wadanda ake tuhumar sun hada da Ministan Kwadago Chris Ngige, da kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami.

An shigar da karar a kotun masana’antu ta kasa da ke Abuja, karar mai lamba NICN/ABJ/269/2022 tana neman kotu ta umarci shugaba Buhari da Mista Ngige su gaggauta aiwatar da dukkan yarjejeniyar da aka kulla da ASUU domin kawo karshen yajin aikin.

Daliban, wadanda suka hada kai wajen shigar da karar sun hada da; Dongo Davou; Oyebode Babafemi; Ejie Kemkanma; Peter Aniefiok; da Imam Naziru. Daliban suna karatun su ne a Jami’ar Jihar Filato, Jami’ar Obafemi Awolowo, Jami’ar Fatakwal, Jami’ar Uyo, da Jami’ar Ibadan, bi da bi.

 Idan za'a iya tunawa a kwanakin baya SERAP  ta shawarci shugaba Buhari da ya kwato naira biliyan 105.7 daga cikin kudin kasar da wasu bata gari suka karkatar yayi amfani da su wajen biyan halaltattun bukatun ASUU.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci