OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

An Tsaurara Tsaro A Majalissa Yayin Da Buhari Ke Gabatar Da Kasafin Kudin 2023

An Tsaurara Tsaro A Majalissa Yayin Da Buhari Ke Gabatar Da

An tsaurara matakan tsaro a kofofin majalisar dokokin kasar nan yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2023 na Naira tiriliyan 19.76.

 An ga wasu jami’an tsaro da suka hada da rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF), DSS, Civil Defence (NSCDC) da kuma Sajan da ke rike da makamai suna sintiri a hanyoyin shiga harabar majalissa.

 ’Yan jarida da aka amince da su ne kawai da kuma muhimman ma’aikatan majalisar aka ba su damar shiga majalissar.

 Zaman, wanda aka fara da karfe 10 na safe a zauren majalisar wakilai na wucin gadi, shi ne na karshe da shugaba Buhari zai gabatar da kasafin.

Shugaban Buhari zai gabatar da kasafin na bana, yayin da ƴan ƙasa ke kokawa da ɗimbin bashin da ƙasar ke ciyowa daga ƙetare da matsin tattalin arziki.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci