OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

An Bukaci INEC Ta Dauki Ma'aikatan Da Suka Dace Gabannin Zaben 2023

An Bukaci INEC Ta Dauki Ma'aikatan Da Suka Dace Gabannin Zab

An bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta dauki kwararrun ma’aikata da zasuyi aikin babban zabe mai zuwa.

Shugaban kungiyar Unified Nigerian Youth Forum (UNYF), Kwamared Abdulsalam Mohammed Kazeem, a lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya a Kaduna, ya kara da yin kira ga INEC da ta kuma tabbatar da isar da muhimman abubuwan da za'a bukata domin kada kuria'a a kan lokaci zuwa kowane lungu da sako na jihar da kasa baki daya.

Kwamared Mohammed ya kuma yi kira ga ‘yan kasa da su tashi tsaye tare da marawa hukumar baya domin ganin an gudanar da zaben 2023 cikin lumana da kwanciyar hankali.

 Sai dai ya yi Allah wadai da kiran da ‘yan adawa ke yi na a gudanar da bincike tare da tsige shugaban hukumar ta INEC tare da karyata jita-jitar da ake ta yadawa na cewa shugaban INEC da tawagarsa ba zasu iya gudanar da zaben bisa gaskiya da amana ba saboda matsin lamba daga jam’iyyun siyasa na hana na'urar BVAS aiki.

 A cewar kwamared din "Ba gaskiya ba ne cewa wani ya tursasa INEC da kuma Farfesa Yakubu Mahmood da su dakatar da amfani da BVAS da suka bullo da shi domin cika alkawarin da shugaban kasar ya yi na gudanar da zabe na gaskiya"

Ya Kara da cewar "Doka ce ta kafa INEC kuma tana da doka da ke jagorantar ayyukanta. Babu wani mutum da zai iya farkawa ya yanke shawarar hana amfani da BVAS lokacin da doka ta ce ayi amfani da shi" 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci