OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ambaliyar ruwa ta janyo asarar rayuka 134 da kadarorin N1.5trn a Jigawa

Ambaliyar ruwa ta janyo asarar rayuka 134 da kadarorin N1.5t

Biyo bayan ambaliyar ruwa a jihar Jigawa, akalla mutane 134 ne suka mutu yayin da sama da Naira tiriliyan 1.5 suka salwanta.

Mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) na ofishin jihohin Kano, Katsina, da Jigawa, Rahman Rihub Mahmud Fara a yau (Asabar).

Namadi ya ce yayin da ruwan ke tafiya zuwa Gabashin jihar, kananan hukumomin Kirikasamma da Birniwa na cikin hatsari.

A cewar sa, yayin da ambaliyar ta shafi mutane 272,189, mutane 76,887 sun rasa muhallen su. 

Ya ci gaba da cewa, ambaliyar ta lalata wani kauye gaba daya tare da yanke wata karamar hukumar da sauran ta hanya.

Daily Trust ta ruwaito cewa Namadi ya ce, ruwan ya tafi da hanyoyi 22 da gadoji 11.

Yayin da yake kiran tallafawa daga gwamnatin tarayya da kuma abokan hulda irin su UNICEF, Namadi ya lura da bukatar kwashe yashi da ke cike madatsun ruwa a jihar.

A nasa jawabin, shugaban hukumar ta UNICEF, Fara ya ce shi da tawagar sa sun kai ziyara ne domin duba irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi a jihar da kuma ganin abin da za a iya yi don taimaka wa al’ummomin da abin ya shafa.

Daga nan sai ya yi kira da a hada kai da gwamnatin jihar Jigawa wajen gudanar da ayyukan taimakon gaggawa domin shirya wa abinda ka iya faruwa nan gaba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci