OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Kungiyar Kiristoci Ta Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Gudanar Da Sahihin Zabe

2023: Kungiyar Kiristoci Ta Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Gudan

Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN reshen jihohin Arewa 19 da kuma babban birnin tarayya, ta sanar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta tabbatar da cewa zaben 2023 zai gudana cikin gaskiya da adalci.

Kungiyar kiristocin ta kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tabbatar da mika mulki cikin kwanciyar hankali a karshen wa’adin sa a 2023, inda ta kara da cewa, zai bar wani wani al’amari mai dorewa.

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Reverend Yakubu Pam da babban sakataren ta, Elder Sunday Oibe da aka fitar bayan taron majalisar zartarwa ta kasa (NEC) na kungiyar a Kaduna.

A cewar CAN, wadanda suka yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa, suna amfani da yunwa a matsayin makami yayin da zaben 2023 ke gabatowa.

Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatoci dukkan matakai da su magance matsalar fatara da yunwa a Najeriya.

“Muna kira ga ‘yan Najeriya da su tabbatar an gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali ba tare da nuna adawa ba. Zabe ba yaki bane. Babu wani dan siyasa da ya cancanci mutuwa. Kada Kowa ya ɗauki doka a hannunsa.

“Dole ne ‘yan siyasa su yi siyasa bisa ka’ida, ba tare da nuna kyama ba. Dole ne shugabannin jam’iyya, masu rike da tuta, ‘yan jam’iyya, magoya baya, da magoya bayansu su gudanar da kansu cikin tsari, su mai da hankali kan yakin neman zabensu, akan yadda suke da niyyar magance dimbin matsalolin da suka addabi kasar nan.

 "Kungiyar CAN ta Arewa kuma tana kira ga matasa da kada su bari wani dan siyasa ya yi amfani da su a matsayin makamin tashin hankali. Ku lura da cewa ‘ya’yan wasu daga cikin wadannan ‘yan siyasa da ke daukar matasa aikin ‘yan daba, suna karatu a kasashen waje. Ya kamata iyaye su ja kunnen ’ya’yansu da kada ‘yan siyasa su dauke su aiki a matsayin ‘yan iska.”
 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci