OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Matasan kungiyar CAN Sun Bukaci Al'umma Su Kare Martabar Kuria'ar Su Yayin Zabe

Matasan kungiyar CAN Sun Bukaci Al'umma Su Kare Martabar Kur

Permanent voters card

Kungiyar matasan kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji bari ayi amfani da su a matsayin ‘yan bangar siyasa a zaben 2023.

Kungiyar ta Kuma Yi kira da su kare kuri’unsu domin nuna muradin jama’a don tabbatar da samun shugaba na gari.

 Shugaban kungiyar YOWICAN na kasa, Belusochukwu Enwere, wanda ya bayar da shawarar a wata sanarwa a ranar Lahadin da ta gabata a Abuja, ya ce kungiyar a matsayinta na mai ruwa da tsaki a harkar zabe za ta fara yakin neman zaman lafiya da kawo karshen tashe-tashen hankula a duk sassan kasar nan.

 Enwere, ya ce tilas ne ‘yan Najeriya su tashi tsaye domin rungumar zaman lafiya ko ta halin kaka domin tabbatar da cigaban kasar.

 A cewar Enwere “Dole ne mu kuma gargadi jam’iyyun siyasa da su bi ka’idojin da shari'ah ta gindaya musu domin gujewa husuma"

 “Yan Najeriya, musamman matasa, ba za su kara yarda a yi amfani da su wajen banga da kashe-kashe ba a wannan lokaci na yakin zabe"

 “Ba za mu iya ci gaba da wannan hanya ba, dole ne mu kare kanmu da kuri’unmu kuma mu tabbatar da zaman lafiya mai dorewa wanda al’ada ce da aka sani a Najeriya."

Enwere ya kuma sanar da cewar kungiyar  YOWICAN, daga yau Litinin 24 ga Oktoba,za ta fara wayar da kan jama'a game da yakin neman zaman lafiya zuwa dukkan shiyyoyi, jihohi, kananan hukumomi da kuma matakin gundumomi domin gudanar da babban zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci