OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Ku Bar ‘Yan sanda Suyi Aikin su Yayin Gangamin Neman Zabe - IGP

2023: Ku Bar ‘Yan sanda Suyi Aikin su Yayin Gangamin Neman

Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), Usman Baba-Alkali, ya bukaci jam’iyyun siyasa da ‘yan siyasa da su bar ‘yan sanda su daidaita kamfen dinsu na zaben 2023.

 

 Baba-Alkali ya yi wannan kiran ne ranar Lahadi a Maiduguri yayin da yake zantawa da manema labarai

 

 Baba-Alkali ya ce an dauki matakin ne domin dakile duk wani abu da zai iya kawo tabarbarewar doka da oda.

 

 “Ina rokon ’yan siyasa da jam’iyyun siyasa da su ba mu damar daidaita jerin gwanonsu da gangamin yakin neman zabensu domin gujewa samun matsala"

 

 Kwamishinan ‘yan sanda ya kara da cewar bawai yana nufin sai an nemi izinin Yan Sanda kafin ayi kamfen ko gangami ba amma  ya bukaci a sanar da Yan Sanda don su ba da tsaro a wurin da kuma gujewa hadewar jam'iyyu biyu wajen taro daya a rana daya.

 

 Yayin da yake ba da tabbacin rundunar ta kuduri aniyar tabbatar da tsaro a zaben, IGP ya ce ba za a amince da amfani da jami’an tsaro na bogi da kowane dan siyasa ko jam’iyya ke yi ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci