OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ku Bada Bayani Ga 'Yan Sanda Ba Jama'a Ba - IGP Zuwa Amurka, Burtaniya

Ku Bada Bayani Ga 'Yan Sanda Ba Jama'a Ba - IGP Zuwa Amurka,

Yayin da ake cigaba da damuwa kan rahotannin harin ta’addanci da ake shirin kaiwa Abuja, babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Alkali Baba Usman ya caccaki Amurka da Birtaniya kan baiwa jama’a irin wadannan bayanai.

 A cewar IGP, sanarwar ta’addancin kwanan nan ya kamata a bai wa ‘yan sanda ba ga ‘yan kasa ba.

 A lokacin da yake kaddamar da ofishin ‘yan sanda da bariki a Ibusa, karamar hukumar Oshimili ta Arewa a jihar Delta, Usman ya bayyana cewa ‘yan sanda na aiki da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da cewa mazauna garin sun samu cikaken tsaro.

 “Ta yaya za ku saki sanarwar tsaro, ba ku sanar da ’yan sanda ba, ku zagaya kuna gaya wa mutanen ku; kar ka je Abuja, ka dawo daga Abuja?

“Idan kana da bayanai kan tsaro, ya dace ka sanar da ‘yan sanda kuma za mu nemo hanyar da za mu magance shi, maimakon kai wa jama’a.

 Muna aiki tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da tsaron mazauna yankin,” in ji shi.

 Kalaman na IGP na zuwa ne bayan da gwamnatocin Amurka da Birtaniya suka fitar da sanarwar tsaro a farkon mako.

 

 Inda sanarwar ta bukaci ’yan kasar da su bar Abuja har sai an magance barazanar ta’addanci.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci