OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: INEC Ta Soke Rajistar Sama Da Mutum Miliyan Biyu

2023: INEC Ta Soke Rajistar Sama Da Mutum Miliyan Biyu

Nigerians are being encouraged to get their PVCs as elections near

Hukumar zabe ta Kasa, INEC tace ta soke rajistar mutum miliyan 2 da dubu dari bakai da aka tabbatar sun yi rajista fiye da sau daya.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya sanar da haka, lokacin da yake jawabi kan mulkin demokraɗiyya da ya gudana a birnin Washington na ƙasar Amurka, ranar Talata.

Farfesa Yakubu ya kara da cewa zuwa watan Nuwamba aluma za su iya karɓar sabbin katunan zaɓen nasu.

Ya ce yanzu haka ma an kammala haɗa kashi 50% na katunan zaɓen, wanda zai bayar da damar yan kasar nan su fara karaba katunan nan ba da jimawa ba.

Da yake Karin bayani kan kalubalen da hukumar ke fuskanta, yace rashin tsaro babbar barazana ce ga zaben badi.

Amma hukumar na tattaunawa da shugabannin tsaro kan lamarin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci