Babban kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta kasa NSCDC, Dakta Ahmed Audi, ya yi alkawarin Ladabtar da duk wani jami’in da aka samu da hannu a cikin satar man fetur a yankin Neja Delta.
Audi ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya ke zantawa da kamfanin dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a birnin tarayya Abuja.
Ya ce rundunar na gudanar da bincike kan rahotannin da ake zargin wasu ma’aikata da hada hannu da barayin mai a yankin Neja-Delta.
Audi ya ce hukumar NSCDC ta inganta tsarinta da ka’idojin aiki, tare da samar da isassun hanyoyin da za a bi wajen binciken dukkan wanda ake zargi.
Audi ya ce hukumar NSCDC ta inganta tsarinta da ka’idojin aiki, tare da samar da isassun hanyoyin da za a bi wajen gudanar da sahihin binciken.
A cewar Dr Ahmed Audi “Zan so na tabbatar wa ‘yan Najeriya da zarar mun kammala bincike, duk wanda aka samu da laifi za a hukunta shi"
0 Tsokaci