OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Zamu Kawo Ƙarshen Rashin Tsaro Nan Da Watan Disamba, Cewar Minustan Cikin Gida

Zamu Kawo Ƙarshen Rashin Tsaro Nan Da Watan Disamba, Cewar

Rauf Aregbesola

Ministan harkokin cikin gida, Mista Rauf Aregbesola, ya bayyana fatansa na ganin cewa an kawo karshen rashin tsaro nan da watan Disamba na wannan shekara.

Aregbesola ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis din da ta gabata yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron Majalisar Tsaron Kasa.

Taron wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja, ya ce nan ba da jimawa ba za a kawo karshen rashin tsaro.

Ministan ya kuma sanar da rusa kwamitin yaki da shigo da makamai ba bisa ka’ida ba, alburusai, makamai masu guba, makamai masu guba da lalata bututun mai wato NATFORCE.

A cewarsa, hukumar ta tsarin ta gamsu da yadda jami’an tsaro ke gudanar da yaki da ta’addanci, yana mai bayyana fatan ganin an kawo karshen kalubalen tsaro nan ba da jimawa ba.

“Majalisar ta kammala taron na yau, Ta samu bayanai daga dukkan shuwagabannin tsaro kuma majalisar ta gamsu sosai da yadda dukkan shuwagabannin tsaron mu suke yi;  sojoji da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro.

"Mun yi farin ciki da rawar da suka taka da kuma nasarorin da aka samu kawo yanzu, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

“Muna saran zuwa watan Disamba, kamar yadda shugaban majalisar, shugaban kasa ya umarta, wanda ya fada wa dukkan ‘yan Najeriya a baya, cewa za mu kawo ƙarshen kalubale na ‘yan fashi musamman, tayar da kayar baya, garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

“Hakazalika, muna jin dadin yadda ‘yan sandan Najeriya suka gudanar da zabukan Anambra, Ekiti da Osun, wanda zaben ya nuna irin jajircewarmu ga dimokuradiyya da kuma bayyana ra’ayoyin jama’a a rumfunan zabe.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci