OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Bama-bamai sun daki sansanin yan gudun hijira a Congo

Bama-bamai sun daki sansanin yan gudun hijira a Congo

Hare-haren bama-bamai da aka kai kan sansanonin 'yan gudun hijira biyu a gabashin Congo ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 12 ciki har da yara kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar. 

Hare-haren bama-bamai sun auna sansanonin da ke Lac Vert da Mugunga, kusa da birnin Goma, kamar yadda aka bayyana a cikin wata sanarwa da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, wadda ta yi Allah wadai da hare-haren a matsayin "cin zarafin bil'adama da kuma dokokin jin kai na kasa da kasa," wanda ke iya zama laifukan yaki. 

A 'yan watannin baya-bayan nan, kungiyar 'yan tawaye da aka fi sani da M23 ta kai farmaki garin Goma da ke gabashin kasar, lamarin da ya sa dubban mutane suka nemi mafaka a sansanin daga yankunan da ke kewaye da su. 

Kungiyar agaji ta Save The Children, ta ce tana nan a daya daga cikin sansanonin lokacin da aka harba abun fashewar ya buhi wata kasuwa dake gabansu

Kungiyar ta bayyana cewa mutane da dama ne suka jikkata, galibi mata da kananan yara, inda har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba. 

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Jean Jonas Yaovi Tossa, ya tabbatar da cewa akalla mutane 12 ne suka mutu yayin da sama da 20 suka jikkata a hare-haren.

 Bayan tashin bama-baman, shugaban kasar Congo Felix Tshisekedi, wanda ke ziyarar kasashen Turai, ya yanke shawarar komawa gida, a cewar wata sanarwa daga ofishinsa.

Tshisekedi dai ya sha zargin Rwanda da hargitsa kasar Kongo ta hanyar tallafa wa 'yan tawayen M23, lamarin da Rwanda ta musanta. 

Masana na Majalisar Dinkin Duniya da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ma sun zargi Rwanda da mara wa 'yan tawaye baya.

 A farkon makon nan ne shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci Rwanda da ta daina goyon bayan kungiyar M23 yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da Tshisekedi a birnin Paris. 

Tashin bama-baman ya biyo bayan mamaye garin Rubaya da kungiyar M23 mai albarkatun ma'adinai a wannan makon.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci