OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Zamfara Ta Sake Rufe Manyan Hanyoyi Bakwai Da Kasuwanni Biyu

Zamfara Ta Sake Rufe Manyan Hanyoyi Bakwai Da Kasuwanni Biyu

Governor Bello Matawalle of Zamfara State

Biyo bayan sabbin hare-haren ‘yan bindiga a jihar Zamfara, Gwamna Bello Matawalle ya amince da rufe wasu manyan tituna 7 da kasuwanni 2.

Kwamishinan yada labarai na jihar Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan.

Dosara wanda ya bayyana hakan a yau, ya ce hakan wani mataki ne na dakile matsalar tsaro a halin yanzu.

Hanyoyin bakwai da aka rufe sun hada da: Colony zuwa Lambar Boko, Titin Bakura zuwa Lambar Damri, Mayanchi - Daki Takwas zuwa titin Gummi, titin Daki Takwas zuwa Zuru, Titin Kucheri- Bawaganga- Wanke, titin Magami zuwa Dangulbi da titin Gusau zuwa Magami.

A cewar kwamishinan, matakin ya zama wajibi ne biyo bayan hare-haren da aka kai wasu kananan hukumomin jihar.

A cewar sa: “Gwamnati ta yi bakin ciki da damuwa game da sake bullar ayyukan ‘yan bindiga da kuma kashe-kashen da aka yi wa wasu mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a kwanakin nan a kananan hukumomin Gusau, Tsafe, Gummi, Bukkuyum, Anka Bungudu, Maru, Maradun da Kaura Namoda.”

Kwamishinan ya ci gaba da cewa, a wani bangare na matakan dakile matsalar tsaro, gwamnan ya kuma amince da rufe kananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Gummi.

Sauran kauyukan da dokar gwamnati na hana zirga-zirgar ta shafa sun hada da: Yarkofoji, Birnin Tudu, Rini, Gora Namaye, Janbako, Faru, Kaya, Boko da Mada.

Dosara ya bayyana cewa: “Daga yanzu an takaita duk wani zirgazirga a kananan hukumomi da garuruwan da aka ambata.

“An umurci jami’an tsaro da su yi rashin tausayi ga duk wanda aka samu da karya dokar.

"Gwamnatin jihar ta kuma duba yiwuwar rufe kasuwannin Danjibga da Bagega."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci