OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Zamfara: Matawalle Na Dab Da Aiwatar Da Mafi Karancin Albashi N30,000

Zamfara: Matawalle Na Dab Da Aiwatar Da Mafi Karancin Albash

Shugaban ma’aikatan jihar Zamfara, Kabiru Gayari ya ce nan ba da dadewa ba gwamna Bello Matawalle zai aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000 ga ma’aikata a jihar.

Gayari ya bayyana haka ne a Gusau yayin taron wakilan kungiyar manyan ma’aikatan Najeriya karo na hudu a jihar.

Gayari wanda ya samu wakilcin babban sakatare na ofishin shugaban ma’aikata, Yusuf Bakura ya ce nan ba da dadewa ba rikicin da ke tsakanin jihar da kungiyoyin kwadago zai zama abin tarihi.

Ya kuma yi kira ga kungiyar da ta kwantar da hankalinta domin shirye-shiryen amincewa ya kai kashi 70 cikin 100.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) a jihar, Sani Halliru ya yi kira ga ma’aikata da su marawa kungiyar baya a fafutukar da suke yi.

Halliru wanda ya samu wakilcin mukaddashin sakataren jihar, Abubakar Gusau ya bukaci ma’aikata da su tallafa wa kungiyar domin ganin an aiwatar da mafi karancin albashin na N30,000.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci