OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan ta'adda sun kai hari a shingen bincike na sojoji, sun kashe wasu a Zuma

'Yan ta'adda sun kai hari a shingen bincike na sojoji, sun k

Wasu ‘yan ta’adda sun kai hari a wani shingen binciken sojoji da ke kusa da Zuma Rock a jihar Neja inda suka kashe wasu jami’ai.

An kai harin ne a daren ranar Alhamis a kusa da garin Zuba da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Rahotanni sun ce, 'yan ta'addan sun kai harin ne da misalin karfe 7 na dare yayin da suka yi harbin kan mai uwa da wabi.

Wata majiya da ta nemi a sakaye sunanta ta bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kai kusan mintuna 30 suna sheke ayar su kafin su kama hanyar Kaduna.

A wani bincike da aka yi, sojoji sun zo wurin da lamarin ya faru ne daga Barikin Sojoji na Zuma mintuna 20 bayan harin sannan suka karbe ikon yankin.

An kuma ga motar ‘yan sanda na sintiri a wurin.

Hakan na zuwa ne bayan barazanar kai hari da ‘yan ta’adda suka yi a kan wasu yankunan babban birnin Tarayya, Abuja.

Idan dai za a iya tunawa, ‘yan ta’addan sun kai hari a wani rukunin jami’an tsaro na soji inda suka kashe manyan jami'ai a Abuja.

Lamarin da ya tilasta wa gwamnatin jihar Nasarawa mai makwabtaka da Abuja rufe dukkan makarantun jihar.

Harin na Zuma ya zo ne sa'o'i kadan bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron tsaro. 

Da yake zantawa da manema labarai bayan taron tsaron, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno ya bayyana halin da kasar ke ciki a matsayin 'mawuyacin hali."

Ya ce, “Shugaban ya kira taron na yau, a ci gaba da taron da aka yi a makon da ya gabata domin tattauna batutuwan tsaro da aka baiwa hukumomin tsaro daban-daban.

“Taron ya tattauna kan dukkan wadannan batutuwa, bayan takaitaccen bayani da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya yi, wanda yawanci shi ne tsarin.

“Har ila yau, majalisar ta ga ya zama dole ta sanar da jama’a, cewa yaki da wannan nau’in rikicin na hadin gwiwa ne.

"Ba wani abu ba ne da ya kamata a bari bane ga jami'an tsaro, leken asiri da masu zartar da doka kawai."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci