OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 11 Watanni da suka shude

‘Yan Sanda Sun Yi Caraf Da Wani Makerin Bam a Taraba

‘Yan Sanda Sun Yi Caraf Da Wani Makerin Bam a Taraba

Nigerian Police

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cafke wani da ake zargin mai kera bam ne a jihar Taraba.

An kama wanda ake zargin ne a ranar Laraba a Tella, karamar hukumar Gassol ta jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Kayayyakin da aka gano a gidan wanda ake zargin sun hada da sassa daban-daban na kera bama-bamai.

AllNews ta tattaro cewa wanda ake zargin ya yi amfani da gidansa ne a matsayin masana’antar sa na bam.

Bayan kama shi, an kuma kwato makamai da alburusai daban-daban kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Duk da cewa ba a bayyana sunan wanda ake zargin ba, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wanda ake zargin dan jihar Zamfara ne.

 A halin da ake ciki kuma an ruwaito cewa yana hannun ‘yan sanda a Jalingo, babban birnin jihar domin ci gaba da bincike.

Ku tuna cewa jihar ta sha fama da hare-haren bama-bamai a cikin watan da ta gabata.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai