OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Da Ya Kashe Iyayen sa A Jigawa

'Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Da Ya Kashe Iyayen sa A Jigaw

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wani matashi mai suna Munkaila Ahmadu mai shekaru 37 bisa zargin kashe iyayen sa a karamar hukumar Gagarawa da ke jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Lawan Shiisu ya fitar ranar Alhamis.

Shiisu ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan da ya kai hari ga iyayen sa da wasu mutane biyu da tabarya. 

A cewarsa, wadanda Ahmadu ya kai wa hari sun hada da, Ahmad Muhammad mai shekaru 70, Hauwau Ahamadu mai shekaru 60, Kailu Badugu mai shekaru 65, da Hakalima Amadu mai shekaru 60.

Shiisu ya kara da cewa an garzaya da wadanda harin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Gumel.

Ya bayyana cewa, sakamakon raunukan da suka samu a harin, iyayen wanda ake zargin, Ahmad da Hauwau sun rasu bayan wani likita a asibitin ya tabbatar da hakan. 

Sai dai sauran biyun na ci gaba da karbar kulawa daga ma'aikatan lafiya. 

A cewar sanarwar, “Yau da misalin karfe 11:30 na safe ne muka samu labarin cewa wani Munkaila Ahmadu da ke kauyen Zarada-Sabuwa a karamar hukumar Gagarawa a jihar Jigawa, ya yi amfani da tabarya inda ya far wa wadannan mutane.

“Ahmadu Muhammad, Hakimin kauyen Zarada-Sabuwa, Hauwa Ahmadu, Kailu Badugu da Hakalima Amadu, duk a kauyen Zarada-Sabuwa a karamar hukumar Gagarawa.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kara da cewa binciken farko ya nuna cewa wadanda suka mutun iyayen wadanda ake zargin ne.

Ya kara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu idan an kammala bincike kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aliyu Tafida ya umarta.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci