OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Yan kasuwa a Legas sun bukaci gwamnati ta sauƙaƙe hanyoyin kasuwanci a kasarnan

 Yan kasuwa a Legas sun bukaci gwamnati ta sauƙaƙe hanyoyi

Kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Legas (LCCI) ta bukataci gwamnatin tarayya ta sassauta hanyoyin kasuwanci domin bunkasa tattalin arzikin kasar. 

 

Shugaban LCCI, Gabriel Idahosa ne ya mika wannan bukata a wani taron manema labarai kan yanayin tattalin arziki da aka gudanar a ranar Alhamis a Legas. 

 

A cewarsa, dole ne gwamnati ta samar da wani yanayi da zai bunkasa fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare, da karuwar kudaden shiga a cikin gida, hadi da kara habaka harkokin kasuwanci. 

 

"Muna ba da shawarar cewa gyare-gyare dole ne ya haɗa da sauƙaƙe da daidaita hanyoyin kasuwanci tare da magance matsalolin da yan kasuwan ke fuskanta kamar fitar da kaya a tashar jiragen ruwa, cunkoso, da farashin sufuri. Ana sa ran wannan zai sanya kasar nan ta zama cibiyar kasuwanci a yankin Afrika "in ji shi.

 

 Dangane da hauhawar farashin kayayyaki da ake ci gaba da samu a kasar shugaban LCCI ya ce ya kamata hukumomin su mai da hankali kan abubuwan da ke haifar da hauhawar farashin kayayyaki ta hanyar bunkasa samar da isasshen kayan a cikin gida.

 

 "Muna kira ga Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya ci gaba da gyare-gyaren fannin hadahadar kasuwar canji (forex) domin karyewar darajar Naira idan aka kamanta da kudaden ketare ne abin da ke haifar da hauhawar farashin kayayyaki.” 

 

Ya kara da cewar ya kamata CBN ya cigaba da samar da manufofi da zasu jawo hankalin alumma su sanya hannun jari a hadahadar kudi a kasar nan.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci