OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Yan Bindiga Sun Saki Limamin Anglican, Matar sa Da Direban Sa

Yan Bindiga Sun Saki Limamin Anglican, Matar sa Da Direban S

'Yan bindiga sun saki babban Limamin cocin Anglican na Jebba dake jihar Kwara, Reverend Aderogba Adeyinka, da matarsa ​​da direbansa.

'Yan bindigan sun sako wadanda aka sacen a ranar Talata.

AllNews ta tattaro cewa an yi garkuwa da Bishop din da mukarrabansa ne a lokacin da suke dawowa daga jihar Ogun ranar Lahadi.

An yi garkuwa da su ne a lokacin da suke gyara motarsu wadda ta samu matsala.

Masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 50 a ranar Litinin.

A halin yanzu dai babu wani bayani ko an biya kudin fansa kafin a sake su.

Hakan ya fito ne ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar kwara, Adewale Osifeso.

Osifeso ya ce an sako wadanda lamarin ya rutsa da su ba tare da wani rauni ba.

Ya ce an samu saukin sakin su ne ta hanyar tura jami’ai a aikin ceto.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ya ce, “Tsarin jami’an ‘yan sanda masu yawa domin gudanar da aikin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su da kuma mamaye yankin baki daya da rundunar ‘yan sandan suka yi ya matsawa masu garkuwa da mutanen wajen kubutar da wadanda abin ya shafa.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci