OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Bindiga Sun Kutsa Kauyukan Filato, Sun Kashe Mutum 5, Sun Sace Shanaye

'Yan Bindiga Sun Kutsa Kauyukan Filato, Sun Kashe Mutum 5, S

Somewhere in Northern Nigeria, villages sacked by bandits during one of their attacks.

Biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Wase da ke jihar Filato, mutane biyar sun mutu yayin da suka yi awon gaba da daruruwan shanaye. 

An kai hare-haren ne a kauyukan Shegyam da Dogon Ruwa na karamar hukumar Wase ta jihar.

AllNews ta tattaro cewa an kai hare-haren ne da safiyar Laraba.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun kai hari kauyen Shegyam inda suka kashe mutane biyu kafin su wuce Dogon Ruwa inda suka kashe wasu uku.

‘Yan bindigan sun kuma tafi da daruruwan shanaye a cewar wani mazaunin garin, Abdullahi Usman, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, DSP Alabo Alfred ya ce ba zai iya tantance hakikanin adadin wadanda suka mutu ba saboda ana ci gaba da bincike.

A halin da ake ciki, ya bayyana cewa rundunar ta samu rahotanni da ke nuni cewa mutum daya ya samu rauni kuma an kai shi asibiti domin kula da lafiyar sa.

Ya kuma kara da cewa da zarar ya samu cikakken rahoton faruwar lamarin, zai sanar da hakan.

Idan dai za a iya tunawa Wase ya ga jerin hare-haren ‘yan bindiga a cikin watannin da suka gabata wanda ya yi sanadin asarar rayuka da asarar dukiyoyi a yankin karamar hukumar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci