OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Yadda Davido Ya Hada Kusan N200m Daga Abokai Da Masoya

Yadda Davido Ya Hada Kusan N200m Daga Abokai Da Masoya

Wani mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido ya samu tallafin kudin da suka kusa Naira Miliyan Dari Biyu cikin wasu sa'o'i kadan.

 

Mawakin wanda yanzu haka yana hutawa a kasar Dubai ya kalubalanci abokansa da magoya bayansa da su tura masa Naira miliyan daya, inda ya ce ya dade yana tallafawa mutane haka kuma yanzu lokaci ne da za'a tallafa masa.

 

Daga lokacin da ya wallafa bayanin nasa a shafin sa na Instagram, ya samu naira miliyan bakwai a cikin mintuna goma.

 

Baya ga haka ne yace dama burin sa taimakon ya kai Naira miliyan dari.

 

Wadanda suka tura taimakon sun hada da hamshakin attajirin dan kasuwa, Femi Otedola da hamshakin attajiri, Obi Iyiegbu wanda aka fi sani da Obi Cubana.

 

Wasu mutane da dama irin su Naira Marley, Zlatan, MC Galaxy, taurarin Big Brother Naija; Nengi da Dorathy ba a bar su a baya ba.

 

Daga lokacin tattaro bayanan wannan rahoto, kudaden sun kai Naira miliyan 134.

 

Mawakin ya kara cewa yanzu tallafin ya koma na naira miliyan dari biyu. 

 

Hakan dai ba shi ne na farko da mawaki ya bukaci tallafi wurin mutane ba.

 

A kwanakin baya an samu wani mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara wanda ya bukaci masoyan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari su tura masa kudi in har suna kaunar sa.

 

Davido dai ya faro abin kamar wasa amma a yanzu ya mamaye yanar gizo da ra'ayoyin jama'a daban-daban.

 

 

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci