OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Dan Mawaki Davido

Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Dan Mawaki Davido

Kakakin yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyi, a safiyar yau Talata, ya tabbatar da cewa dan mawaki Davido, Ifeanyi ya rasu.

 

Labari mai ban tausayi na rasuwar dan mawakin ya yadu a shafukan sada zumunta da yammacin ranar Litinin bayan da jaruma Eniola Badmus ta wallafa a shafinta na Instagram. Daga baya ta goge sakon.

 

A wata tattaunawa da ya yi da PREMIUM TIMES ta wayar tarho da safiyar Talata, Hudeyin ya ce an kama wasu daga cikin hadiman mawakin da maaikatansa.

 

Ya ce: An kama ma'aikatan su takwas domin a yi musu tambayoyi.

 

Bai bayyana wurin da aka kai su ba saboda yana fargabar mutane sun cimma wurin.

 

Rahotanni sun ce yaron mai shekaru uku ya nutse ne a cikin kogin wanka da ake kira swimming pool a gidan su da ke Legas kuma ya dade a ruwa na tsawon wani lokaci da ba a tantance ba kafin aka farga.

 

An garzaya da shi asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci