OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Atiku Shine Zaɓin Mutanen Osun, Cewar Zaɓaɓɓen Gwamna Adeleke

Atiku Shine Zaɓin Mutanen Osun, Cewar Zaɓaɓɓen Gwamna Ad

Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya bayyana cewa al'ummar jihar Osun za su zaɓi Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Adeleke yayi wannan bayani ne a yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jihar, inda ya ce ƴan Najeriya sun yi watsi da jam’iyyar APC.

Da yake yabawa mazauna Osun bisa nuna ƙauna da haɗin kai a lokacin zaɓen gwamna, Adeleke ya ce har yanzu burinsa bai cika ba, har sai shugaban Najeriya na gaba ya fito daga PDP.

“A matsayina na gwamnanku a jihar Osun, ina buƙatar ɗan takaran mu a matakin tarayya da ya ba ni goyon baya yayin da nake gabatar da ajandar mu biyar ga mutanen jihar Osun.  

"Kasancewar Atiku a takaran shugaban ƙasa za ta ƙara wa jiharmu ƙarfin gwiwa tare da taimaka mana wajen shawo kan dimbin ƙalubalen da ke fiskantar mu.

“Najeriya na buƙatar shugabancin Atiku saboda yana da mafi ƙwarewa a cikin dukkan masu neman shugaban ƙasa.

“Ƙudurorinsa na Najeriya ya yi daidai da muradin ƴan Osun na sake fasalin ƙasar, da kuma samar da ƴancin cin gashin kan kananan hukumomi, yaƙk da cin hanci da rashawa, samar da ingantattun ababen more rayuwa.

"Sa'annan haɗin kan kasa a bangarori daban-daban da kuma samar da shugabanci na gari.

“Aikinmu shi ne bayar da dukkanin ƙuri’un Osun na wa Atiku da Okowa, abu ne mai yiwuwa kuma dole ne mu yi".

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci