OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Adeleke a Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Osun

Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Adeleke a Matsayin Ɗan Takarar G

Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da Ademola Adeleke a matsayin ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, gabanin zaben gwamnan jihar Osun. 

Kotun ta bayyana haka ne a ranar Alhamis, yayin da ta yi watsi da ƙarar da wani tsohon dan takara, Oyedotun Babayemi ya shigar.

Babayemi wanda ya nemi a bayyana shi a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar da akayi a ranar 16 ga watan Yuli.

Mai shari’a Amina Augie ya tabbatar da Mista Adeleke a matsayin sahihin zaɓaɓɓen ɗan takarar PDP a zaɓen da aka gabatar.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Kwamitin ya yanke hukuncin cewa an hana shari’ar ne bayan an shigar da ita a cikin wa’adin kwanaki 14 da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Kundin daukaka kara wanda kamar yadda sashe na 285(11) na kundin tsarin mulkin ƙasar Najeriya ya tanadar.

Sa'annan a karo na biyu da aka shigar da ƙaran, kotun ƙolin bata da hurumin sauraron ƙaran, a cewar kwamitin.

A dalilin haka, mai shari’a Augie ya yi watsi da karar da aka shigar na rashin dacewa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci