OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Wani Matashi Ya Mutu A Ruwa Yayin Ceto Saniya a Jigawa

Wani Matashi Ya Mutu A Ruwa Yayin Ceto Saniya a Jigawa

Drown

Wani Adamu Musa da ke Unguwar Magaji a karamar hukumar Buji a jihar Jigawa ya nutse a cikin wani tafki a lokacin da yake ceto saniyar sa da ta fada cikin tafkin. 

Musa mai shekaru 18 a duniya yana kiwo a kusa da yankin lokacin da lamarin ya faru.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya reshen Jigawa, CSC Adamu Shehu ya fitar a ranar Lahadi. 

A cewar Shehu, lamarin ya faru ne da misalin karfe 2 na yammacin ranar Asabar lokacin da matashin ya dauki shanayen sa guda biyu domin kiwo.

Ya kara da cewa daya daga cikin shanun ta fada cikin wani tafki da ke kusa da wajen kiwon wanda hakan ya sa Musa ya fada ceto ta.

Sai dai abin takaicin shi ne matashin ya nutse kuma ba a same shi ba sai da karfe 1 na safiyar Lahadi ta hanyar hadin gwiwa da jami’an tsaron farin kaya da mazauna yankin suka yi.

A cewar sanarwar: “An yi nazari sosai kan gawar, aka tabbatar da mutuwar sa sannan aka mika wa iyayen sa domin su yi musa jana’iza yadda ya kamata, yayin da aka ceto saniyar da rai."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci