OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

APC Ta Dakatar Da Shugaban Ta Na Kasa Abdullahi Umar Ganduje

APC Ta Dakatar Da Shugaban Ta Na Kasa Abdullahi Umar Ganduje

Kano Governor, Abdullahi Umar Ganduje

Ofishin mazabar Ganduje dake karamar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano sun dakatar da Abdullahi Ganduje, shugaban jam’iyyar APC na kasa. 

 

Majalisar zartarwar mazabar Ganduje karkashin jagorancin Haruna Gwanjo ce ta sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Kano a ranar Litinin. 

 

Gwanjo ya bayyana cewa dole ne tsohon gwamnan ya wanke sunansa daga zargin cin hanci da rashawa da ake masa sanadiyar bediyon dala da aka dade ana zarginsa da shi.

 

Wannan na zuwa a daidai lokacin da wata babbar kotun jihar Kano ta sanya ranar da za a gurfanar da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje da matarsa Hafsat Ganduje a gaban kuliya.

 

Ma'auratan za su fuskanci tuhumar cin hanci da rashawa da sayar da kadarorin gwamnati ba bisa ka'ida ba a ranar 17 ga Afrilu, 2024. 

 

Ganduje yana fuskantar akalla tuhume-tuhume guda 8 da gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta shigar da shi.

Masu gabatar da kara sun yi zargin cewa ma'auratan tare da wasu mutane shida suna da hannu a "a cin hanci da rashawa, da almubazzaranci da dukiyar jama'a, Hadi da karkatar kudaden da suka kai dala 413,000 da kuma Naira biliyan 1.38." Kamar yadda takardar kotun ta bayyana.

Sauran wadanda ake kara tare da ganduje sun hada da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd da Lesage General Enterprises.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci