OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Watanni da suka shude

Sojoji Sun Ƙara Ceto Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok Da Ƴaƴan Ta Huɗu

Sojoji Sun Ƙara Ceto Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok Da

Photo Source: Daily Post

Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarun tasun ceto ɗaya daga cikin ƴan matan makarantar Chibok da ƴan bindiga suka sace a shekarar 2014.

Yarinyar da aka ceto mai suna Yana Pogu, ta samu nasarar kubuta ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata a Borno. 

Dakarun sojojin Najeriya karkashin Operation Hadin Kai sunce sun ceto yarinƴar ne da ƴaƴanta huɗu, wadda ta haifi ƴan biyu daga cikinsu wata huɗu daya wuce.

 Pogu, wacce aka ceto tare da ‘ya’yanta hudu, ta haifi wasu tagwaye watanni hudu da suka wuce.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa Sojojin Najeriya ne da ke samun goyon bayan wani ginshikin rundunar hadin gwiwa ta Civilian Joint Task Force (CJTF) suka samu nasarar ceto ta a lokacin da suka kai farmaki a unguwar  ƴan ta’addan a karamar hukumar Bama, jihar  Borno.
 
A cewar majiyoyin leken asiri, sojojin sun yi artabu tare da fatattakar ƴan ta’addan, inda suka kashe ƴan ta’adda da dama a farmakin, yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga.

“A yayin harin, sojoji sun yi nasarar kubutar da Yana Pogu, ƴar Chibok, wacce ke lamba 19 a jerin yaran matan Chibok,  tare da ƴaƴanta hudu,” inji majiyar.

“An same ta da wasu tagwaye ƴan watanni huɗu a cikin wani yanayi mara kyau".

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai